Iran sun ci gaba da kai wajuna hari da makamai masu linzami
Donald Trump ya buƙaci mazauna Teheran da su fice daga babban birnin na Iran, lamarin da ya haifar da shakku kan musanta yiwuwar shigar Amurka yaƙin na Isra’ila da Iran kai-tsaye.
Haka na zuwa ne yayin da Isra’ila da Iran sun ci gaba da kai wa juna farmaki da makamai masu Linzami, kwana biyar bayan ɓarkewar yaƙi tsakaninsu, lamarin da ya ƙara fargabar da ake ciki kan ƙazancewar yaƙin tsaknain ƙasashen biyu.
Hare-haren da ake ci gaba da kai wa juna tsakanin Isra’ila da Iran a Talata na zuwa ne sa’o’i bayan da shugaba
Tuni dai shugabannin ƙasashen ƙungiyar G7 suka buƙaci gaggauta ɗaukar matakan dakatar da rikicin da ke neman ƙazancewa a Yankin Gabas Tsakiya ciki har da ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, sai dai basu ambaci cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Iran ba.
A baya bayan nan ne dai Isra’ila ta yi iƙirarin kashe wani ƙarin Janar ɗin sojan Iran, abinda ya sa adadin manyan Kwamandojin da suka rasa rayukansu kaiwa aƙalla 11. Sai dai har yanzu Iran ba ta ce komai kan iƙirarin na Isra’ila ba.
Rahotani sun ce Isra’ilar ta faɗaɗa hare-hare ta sama da take kai wa a sassan birnin Teheran, yayin da ita kuma Iran ta sanar da samun nasarar lalata muhimman wuraren sojin Isra’ila ciki har da ma’aikatar leƙen asirin ƙasar a yayin hare-haren da ta kai ɗazu. Rahotanni dai na cewa Iran ɗin ta sake harba makamai masu linzami da dama kan Isra’ila.
