Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya gaggauta tallafa wa al’ummar Shuwaki da ke karamar hukumar Tudun Wada, bayan ambaliyar ruwa ta lalata gonakin shinkafa sama da 200 tare da lalata muhimman ababen more rayuwa.
An yi wannan kiran ne a zaman majalisar na ranar Litinin, wanda Kakakin Majalisar, Jibril Falgore, ya jagoranta.
Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Tudun Wada, Sule Shuwaki, ya ce ruwan sama mai karfi da aka samu ranar Alhamis ya haddasa ambaliyar ruwa mai tsanani a yankin.
Ya ce gonakin shinkafa sama da 200 na manoman yankin sun lalace, yayin da ambaliyar ta kuma kwashe wata gada mai tarihi da ke kan hanyar Tudun Wada zuwa Shuwaki.
“Ruwan sama da aka yi ranar Alhamis ya lalata gonakin shinkafa sama da 200 sakamakon ambaliyar ruwa a Shuwaki. Ambaliyar ta kuma kwashe wata gada da ke kan hanyar Tudun Wada zuwa Shuwaki,” in ji Sule Shuwaki.
Dan majalisar ya ce lalacewar gadar ta kawo cikas ga harkokin tattalin arziki a yankin, tare da wahalar da mazauna wajen zuwa gonakinsu da zirga-zirga tsakanin al’ummomin da lamarin ya shafa.
Ya bukaci gwamnati da ta gaggauta samar da kayan tallafi da sauran agajin da manoma da mazauna yankin da ambaliyar ta shafa ke bukata.
“Muna rokon gwamnatin jihar da ta taimaka wa manoman da abin ya shafa da sauran mazauna yankin da ambaliyar ta shafa, domin rage musu radadin da suke ciki,” in ji shi.
Sule Shuwaki ya kuma bukaci a gaggauta gyara gadar da hanyar, domin rage wahalhalun da mazauna Shuwaki da makwabtansu ke fuskanta.
Dan majalisar Gezawa, Abdullahi Kara, ne ya marawa kudirin baya. Bayan muhawara, majalisar ta amince da kudirin tare da kira ga gwamnatin jihar da ta dauki matakin gaggawa kan matsalar.
