Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada kudirinta na shawo kan matsalar samar da ruwan sha a fadin jihar.
Kwamishinan Ruwa na Jihar Kano Alhaji Haruna Doguwa ne ya bayar da tabbacin hakan a yayin wata ziyarar duba aiki a matatar ruwan Joda dake ka Karamar Hukumar Gabasawa ta jihar.
A inda ta samar da sabon injin da zai rika tura ruwa daga madatsar zuwa kananan hukumomin Gabasawa da Gezawa da kuma wasu sassan unguwannin Nasarawa da ‘Yan Kaba.
Hakaan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in yada Labarai na Yankin Gezawa Jamilu Mustapha Yakasai ya fitar a ranar Talata.
“Gwamnatin tana kokari matuka wajen magance matsalar karancin ruwa tare da tabbatar da wadataccen ruwan sha ga jama’a.
“Sauran matatun ruwa a fadin jihar za mu ci gaba da gyare-gyare domin inganta rabon ruwa”. In ji Kwamishinan.
Doguwa ya tabbatar wa da mazauna kananan hukumomin da abin ya shafa cewa nan ba da jimawa ba za su fara samun ruwa a yankunansu.
