Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da baiwa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnatinsa goyon baya, yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.
Gwamnan ya yi wannan kiran ne yayin da ya halarci taron Maukibi Kadiriyya na bana wanda ya haɗa manyan malamai, ’yan siyasa da sauran manyan baƙi.
Gwamnan ya ce taron ya kasance wata dama ta ƙara ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da fahimtar juna, tare da nuna goyon baya ga jagorancin Shugaba Tinubu.
A yayin taron, an ƙaddamar da wani sabon ginin Maukibi da Gwamnatin Kano ta samar, wanda wakilin Shugaba Tinubu, Hon. Ibrahim Kabir Masari, ya ƙaddamar.
Taron ya kuma samu halartar tsohon Gwamnan Zamfara kuma Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen APC, Abdul’aziz Yari, da tsohon Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.
