Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMataimakin shugaban kasar Kashim Shettima zai bar Najeriya a wannan Laraba domin...

Mataimakin shugaban kasar Kashim Shettima zai bar Najeriya a wannan Laraba domin wakiltar shugaba Bola Tinubu a taron shugabannin kasashen G77 a birnin Havana na kasar Cuba, wanda zai gudana daga ranar 15 zuwa 17 ga watan Satumba.

Date:

Daraktan yada labarai na ofishin mataimakin shugaban kasa, Olusola Abiola, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce Shettima zai bi sahun sauran shugabannin duniya ciki har da babban sakataren majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres a wajen taron.
Ya ce taron zai tattauna batutuwan ci gaban da mambobin kungiyar ke fuskanta, musamman daga kudancin duniya.
Taken taron shi ne Kalubalen Ci gaba na Yanzu: Matsayin Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙira.
Najeriya ta kasance daga cikin mambobin da suka kafa kungiyar G77 da kasashe masu tasowa 77 suka kafa a shekarar 1964.
Kashim Shettima zai samu rakiyar ministan noma da raya karkara Abubakar Kyari, da takwaransa na kere-kere, kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, da kuma babban sakataren ma’aikatar harkokin waje, Mista Adamu Lamuwa

Latest stories

Related stories