Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta yi gargadin cewa...

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta yi gargadin cewa akwai fargabar garuruwa 50 a jihohin kasar nan 13 su fuskanci ambaliyar ruwan mai yawa tsakanin 13 zuwa 17 ga Satumbar da muke ciki.

Date:

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta yi gargadin cewa akwai fargabar garuruwa 50 a jihohin kasar nan 13 su fuskanci ambaliyar ruwan mai yawa tsakanin 13 zuwa 17 ga Satumbar da muke ciki.
Jami’in tsare tsare na hukumar Ibrahim farinloye ya sanar da hakan cikin wata sanarwa ranar larabar 12 ga wannan watan, yace cikin garuruwan da ambaliyar za ta shafa har da karamar hukumar Sumaila da Kunci a nan Kano.
Akwai kuma garuruwan Dutse, Gumel da Gwaram a jihar Jigawa.
Farinloye ya kara da cewa akwai garin Argungu dake jihar Kebbi, sai Kaita, Boindawa Jibia su kuma a Katsina.
Ragowar jihohin sun hada da Zamfara, Bauchi Yobe Taraba da sauran su.
Ahmad Isah shi ne jami’in hulda da jama’a na hukumar kula da Ibtila’I da bayar da agajin gaggawa na Kano zantawar sa da Faisal Abdullahi Bila, yace duk da cewa wata ambaliyar babu yadda za ai da ita, amma akwai sakacin al’umma a yawancin lokuta.

Ya kuma ja hankalin al’umma kan yadda ake zubar da shara a in da bai kamata ba wanda hakan ke jawo ambaliyar ruwan.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories