Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiNajeriya ta rasa matakin farko na kasashen Nahiyar Afirka da su ka...

Najeriya ta rasa matakin farko na kasashen Nahiyar Afirka da su ka fi samar da man A yanzu.

Date:

Najeriya ta rasa matakin farko na kasashen Nahiyar Afirka da su ka fi samar da man A yanzu.
Libya ta karbe matakin farko yayin da Angola ta kasance na biyu a jerin kasashe mafi samar da mai.
Najeriya na daga cikin kasashen da ke ba da gudunmawa wurin samar da mai a duniya duba da tarun arzikin kasar na mai.
Nahiyar Afirka na ba da gudunmawar fiye da kaso 8 na mai a duniya, amma farkon 2023, an samu matsaloli da dama.
Rahoton Energy Chamber ya ce daga watan Janairu zuwa Mayu Nahiyar ta yi asarar fiye da gangan mai dubu 180 a ko wace rana.
Najeriya ta rasa matakin farko a Nahiyar wacce ta fi kowa kasa samar da mai bayan samun matsalolo masu tarin yawa da su ka hada da satar mai din musamman a jihohin Kudu maso Kudu.
Kasar ta fado har mataki na uku bayan Libya da Angola sun karbe matakin farko da na biyu a Nahiyar a matsayin mafi samar da man.
Kasar nan dai ta yi asarar fiye da gangan mai dubu 165 a rana cikin watanni biyar na farkon shekarar 2023.

Latest stories

Related stories