Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Tuesday, May 7, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAddiniManiyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Date:

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya zuwa kasa mai tsarki, hukumar aikin hajj ta kasa tace tana samun nasara a jigilar alhazan.

Hakan na kunshe cikin sanarwar da mataimakiyar daraktan yada labarai da hulda da jama’a ta hukumar Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu.

Usara ta ce a yanzu haka anyi sawu sama da 42 da alhazan Najeriya zuwa kasa mai tsarki.

Tace tuni aka kammala jigilar alhazan jihohin Plateau, Benue da kuma Nasarawa.

Ta kara da cewa a wannan sheka Nahcon ta kara adadin yawan jiragen da za su yi jigilar alhazan Najeriya zuwa kasa mai tsarki zuwa guda 5 domin samun nasarar gudanar da aikin hajj wannan shekara ta 2023 cikin nasara.

Usara, ta ce shugaban hukumar aikin hajji ta kasa alhaji zikrullah kulle hassan, ya bayyana lamarin da ya faru da jirgin da ya dauki alhazan jihar jigawa zuwa kasa maitsarki da ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman malam aminu kano, a matsayin lamari ne daga allah.

Kulle hassan, ya ce Nahcon za ta cigaba da aiki tukuru wajen ganin alhazan da za su sauke farali a wannan shekara basu samu jinkiri ko an sauya musu ranar tafiya ba.

A yanzu haka dai sama da maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki .

Latest stories

Related stories