Majalisar Wakilai ta Tarayya ta gayyaci Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu, tare da Darakta Janar na Ofishin Kasafi na Tarayya, domin su yi bayani kan yadda aka ware fiye da naira biliyan 1 da miliyan 300 ga wata hukuma da ake zargin ba ta da sahihanci.
Matakin na majalisar ya biyo bayan amincewa da wani kudirin gaggawa da ɗan majalisa Yusuf Gagdi ya gabatar a zaman majalisar.
A cikin kudirin, Gagdi ya nuna damuwa cewa sanya kuɗi ga hukumar PFIPC a cikin kasafin kuɗi na nuna akwai gibi a tsarin tsara kasafi da kuma rashin ingantaccen bincike kafin shigar da hukumomi cikin tsarin gwamnati.
A sakamakon haka, majalisar ta amince da kafa wani kwamitin wucin gadi da zai gudanar da cikakken bincike kan yadda aka shigar da wannan hukuma cikin kasafin kuɗin shekarar 2026.
