Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci malamai da masu rike da sarautun gargajiya su ƙara mayar da hankali wajen yi wa jihar da Najeriya baki ɗaya addu’o’in neman zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba, musamman yayin da ake shirin gudanar da zaɓe a faɗin ƙasar.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya halarci zikirin ƙasa da aka gudanar a fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sunusi II.
Gwamna Abba ya ce addu’a na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma, tare da jaddada cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da haɗa kai da malamai da shugabannin gargajiya domin tabbatar da zaman lafiya da bunƙasa ci gaban Kano.
Shugaban Majalisar Shurar Darikar Tijjaniyya, Sheikh Sani Shehu Maihula, wanda dan uwansa kuma kakakin majalisar, Sheikh Ibrahim Shehi Maihula, ya wakilta, ya ce mambobin majalisar sun cimma matsayar marawa Gwamna Abba Kabir Yusuf baya domin sake tsayawa takara.
Ya ce sun dauki matakin ne saboda yadda gwamnan ke tafiyar da mulki, bunkasa al’amuran addini da kuma aiwatar da manufofin da suka shafi jin dadin al’umma.
A nasa jawabin, mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sunusi II, ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da zama masu haƙuri, haɗin kai da mutunta juna, tare da kaucewa duk wani abu da ka iya haddasa rikici kafin, lokacin da kuma bayan zaɓe.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa Zikirin ya samu halartar manyan malamai, masu rike da sarautun gargajiya, jami’an gwamnati da ɗimbin al’umma, daga sassa daban daban na Najeriya, inda aka gudanar da addu’o’i na musamman domin zaman lafiya, haɗin kai da cigaban Kano da Najeriya baki ɗaya.
