Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya, FIFA, Gianni Infantino, ya kai ziyara jihar Delta da ke kudancin Najeriya domin duba ayyukan gyaran filin wasan Warri City Stadium, tare da ƙarfafa shirye-shiryen bunƙasa ƙwallon ƙafa daga matakin ƙananan hukumomi da makarantu.
Infantino ya isa filin jirgin saman Osubi da ke Warri a ranar Juma’a, inda Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da tsohon shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya, Amaju Pinnick, suka tarbe shi.
Ziyarar ta kasance wani ɓangare na ƙoƙarin inganta kayayyakin wasanni da samar da damammaki ga matasa masu sha’awar ƙwallon ƙafa, musamman a makarantu da ƙananan al’ummomi.
A yayin ziyarar, Infantino ya kai ziyara makarantar Hussey College da ke Warri, wadda ta yi suna wajen samar da ƙwararrun ‘yan wasan ƙwallon ƙafa.
Amaju Pinnick ya bayyana cewa makarantar, wadda aka kafa a shekarar 1947, ta samar da ‘yan wasa 17 da suka taɓa wakiltar Najeriya a babbar tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasar, Super Eagles.
Da yake magana da tashar Arise News, Infantino ya jaddada cewa manufar FIFA ita ce tabbatar da cewa kowa ya samu damar shiga harkokin ƙwallon ƙafa, ba tare da la’akari da wurin da yake zaune ba.
Ya kuma yaba wa tawagar ‘yan mata ‘yan ƙasa da shekara 17 ta Najeriya bisa rawar da ta taka a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Morocco, yana mai jaddada muhimmancin ci gaba da tallafa wa matasa maza da mata wajen haɓaka ƙwarewarsu.
A halin yanzu, gwamnatin jihar Delta na gudanar da ayyukan inganta filin wasan Warri City Stadium, waɗanda suka haɗa da gyaran filin ƙwallon ƙafa, wuraren motsa jiki, tafkin ninkaya da ɗakunan sauya kayan ‘yan wasa.
