
Aminu Abdullahi Ibrahim
Hukumar NAFDAC, ta kafa wata rundunar aiki mai mambobi bakwai a Jihar Kano domin yaƙi da yaduwar magungunan jabu da kuma abinci marasa inganci ranar Talata.
Rundunar za ta yi aiki ƙarƙashin sashen bincike da tabbatar da doka na hukumar a matsayin wani reshe na gwamnatin tarayya.
NAFDAC Na Cigaba Da Saka Ido Kan Magungunan Da Aka Soke Lasisinsu
A nasa jawabi, Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Umar Ibrahim, ya ce kafa wannan runduna ya zama dole saboda ƙaruwa da ake samu na amfani da miyagun ƙwayoyi da kuma yaduwar kayayyakin jabu a jihar.
Ya bayyana cewa shaye-shaye na daga cikin manyan matsalolin zamantakewa, musamman a tsakanin matasa da suka fi kaso 70 na al’ummar jihar.
A nasa jawabin, Shugaban rundunar, Kamilu Mudi-Salisu, ya tabbatar da aniyar su na yaƙi da yaduwar magungunan jabu da abinci marasa inganci.
Ya kuma roƙi jama’a da su bai wa wannan shiri goyon baya ta hanyar kai rahoton duk wani abu da ake zargi a cikin al’umma.
Rundunar ta ce za ta riƙa tattara bayanan sirri, sa ido, gudanar da samame, ƙwace kayayyakin haram, kama masu laifi tare da gurfanar da su a gaban kotu, sannan ta wayar da kan jama’a domin dakile yaduwar kayayyakin jabu.
