
Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bayyana cewa yanzu shi “ɗan siyasa ne mai zaman kansa” wanda ba shi da wata alaƙa da jam’iyar siyasa.
Bala Mohammed ya yi wannan furucin ne a lokacin da yake karbar bakuncin jigo a jam’iyyar African Democratic Congress, Peter Obi, tare da masu ruwa da tsaki na Kudu maso Gabas a Bauchi, ranar Alhamis.
Jam’iyyar APC ta ce manyan ‘yan adawa da ke cikin ADC, ba su da wani tasiri a siyasance.
A cewar rahoton Daily Trust gwamnan ya bayyana ganawar tasu a matsayin wani bangare na tattaunawa kan hadin kan kasa da hadin gwiwar siyasa.
Babu wata yarjejeniyar siyasa da za ta iya cire Sarki Aminu – Babba Danagundi
”PDP ko ADC babu wacce ke tsaye da kafarta. Ni ɗan siyasa ne mai zaman kansa yanzu.
Ya ce ita kanta jam’iyyar Peter Obi tana cikin rudani.
Tabbas, dukkanmu muna cikin ‘yan adawa, kuma shi ya sa na ce wannan tattaunawa ce ta siyasa. Ba za mu bayyana duk abin da muka tattauna ba” in ji gwamnan.
Ya bayyana ziyarar Obi a matsayin alama ta kokarin da ake yi na dinke barakar da ke tsakanin yankuna Najeriya da kuma inganta hadin kan kasa.
Tun da farko, Obi ya ce sun kai ziyarar da nufin inganta hadin kai da kuma karfafa hadin gwiwa a fadin kasar.
