Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama mutane shida da ake zargi da hannu a harin da ’yan daba suka kai kasuwar sayar da wayoyi ta Farm Centre, bayan rikicin da ya barke a unguwar Gyadi-Gyadi a ranar Litinin.
wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Litinin 27 ga Afrilu, 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa rundunar ta samu kiran gaggawa da misalin karfe 1:20 na rana, inda aka sanar da cewa wasu da ake zargin ’yan daba sun taru domin tada rikici a Gyadi-Gyadi.
Sanarwar ta kara da cewa ana ci gaba da bincike domin kamo sauran wadanda suka tsere.
Haka kuma, Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya jaddada cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya a jihar ba, tare da yin alkawarin cewa duk masu aikata daba za su fuskanci hukunci bisa doka.
