
Aminu Abdullahi Ibrahim
Ƙungiyar likitocin da ke aiki a asibitocin gwamnatin Jihar Kano ta yi barazanar shiga yajin aikin gargaɗi na tsawon makonni biyu, daga ranar 25 ga Oktoba, 2026, saboda rashin cika buƙatunta da ta ce gwamnati ta yi.
Jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar, NAGGMDP reshen Kano, Dakta Ibrahim Gabari, ne ya bayyana hakan a wata hira da SolaceBase ta yi da shi ranar Laraba.
Dakta Gabari ya ce matakin ya biyo bayan wa’adin da ƙungiyar ta sha bai wa gwamnati, da kuma yarjejeniyar da suka cimma a watan Yuni, wadda ya ce har yanzu ba a aiwatar da ita ba.
Ya bayyana cewa ƙungiyar ta daɗe tana neman ƙarin albashi tun shekarar 2024. A cewarsa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da ƙarin albashin, amma har yanzu ba a aiwatar da shi ba.
Dakta Gabari ya kuma musanta rahotannin da ke cewa an daidaita albashin likitocin jihar da na takwarorinsu da ke aiki ƙarƙashin gwamnatin tarayya.
Ya ce ƙungiyar na kuma neman ɗaukar ƙarin ma’aikatan lafiya, biyan albashi da alawus-alawus da ake bin ma’aikata, samar da kuɗin horar da likitoci ƙwararru, inganta kayan aiki da kuma ƙara tsaro ga ma’aikatan lafiya.
Ya ce ƙungiyar ta tattauna da kwamishinan lafiya na jihar, sannan ta sake ba gwamnati wa’adin makonni uku bayan wani taron ƙungiyar, amma a cewarsa, har yanzu ba a magance matsalolin ba. Ya yi gargaɗin cewa ba za su ƙara amincewa da jinkiri ba.
