Lauyoyin tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, sun bai wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) wa’adin kwanaki uku da ta sanya sunansa a matsayin ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar PDP a zaɓen shekarar 2027.
A cikin wasiƙar da suka aika wa hukumar, lauyoyin sun bayyana cire sunan Pantami daga jerin ƙarshe na ‘yan takara da INEC ta wallafa ranar 10 ga Oktoba, a matsayin abin da ya saɓawa doka kuma ba tare da wani bayani ba.
Lauyoyin sun buƙaci INEC da ta gaggauta wallafa sunan Pantami a matsayin ɗan takarar PDP, tare da yaɗa sunansa da irin muhimmanci da matsayin da aka ba sauran ƴan takara, kafin ranar Laraba, 14 ga Oktoba, 2026.
Sun kuma yi nuni da cewa rashin sanya sunansa a cikin jerin ƴan takarar na iya tauye haƙƙinsa na siyasa da kuma na jam’iyyar PDP, idan har ba a gyara lamarin cikin wa’adin da aka bayar ba.
Ya zuwa yanzu, babu wani martani daga hukumar zaɓe INEC kan wannan buƙata.
Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya zama ɗan takarar gwamnan jihar Gombe na jam’iyyar PDP ne a wani sabon zaɓen fidda gwani da aka gudanar ranar 29 ga Satumba, 2026, bayan wata Babbar Kotun Tarayya ta soke nasararsa ta farko tare da umartar jam’iyyar da ta sake gudanar da zaɓen cikin kwanaki 30.
