Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa na shirin gudanar da wani taron gaggawa a birnin Alkahira yau Talata, domin tattauna batun samar da kariya ta ƙasa da ƙasa ga Falasɗinawa, yayin da hare-haren tashin hankali ke ƙaruwa a yankin.
Wakilin Falasɗinu na dindindin a Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa, Ambasada Mohannad Al-Aklouk ne ya gabatar da buƙatar gudanar da taron.
Ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Falasɗinu na Wafa cewa hare-haren Isra’ila wani tsari ne na kai hare-hare da nufin tilasta wa al’ummomin Falasɗinawa barin yankunansu, faɗaɗa matsugunan ’yan mulkin mallaka, da kuma raunana shirin samar da ƙasashe biyu masu zaman kansu.
Al-Aklouk ya ce hare-haren da ake kai wa a Yammacin Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye na ƙara zama masu tsari da haɗin gwiwa.
Ya bayyana cewa hakan na nuna “wani mataki mai matuƙar haɗari a cikin yaƙin da gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da yi kan al’ummar Falasɗinu da kuma ƙasarsu”.
Ya ƙara da cewa ana buƙatar ɗaukar matakan hukunta Isra’ila ciki har da kakaba takunkumi kan shugabannin Isra’ila, domin kare al’ummar Falasɗinu.
