
Majalisar ƙasa ta gabatar da sabon shirin da ke neman sauya lokacin zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnoni na 2027 zuwa watan Nuwamba 2026, maimakon watan Fabrairu ko Maris kamar yadda aka saba.
Wannan mataki yana cikin gyaran dokar zaɓe ta 2022, wanda ya tanadin cewa za a iya gudanar da zaɓe kafin kwanaki 185 da ƙarewar wa’adin gwamnati mai ci, wanda ke ƙarewa a ranar 29 ga Mayu.
Manufar shirin shine, samar da isasshen lokaci don kammala dukkan ƙorafe-ƙorafen dake gaban kotunan zaɓe kafin rantsar da sabbin shugabanni.
A yayin taron jin ra’ayoyi da kuma kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Dattijai da ta Wakilai kan harkokin zaɓe suka gudanar a jiya Litinin, an bayyana cewa sabon tsarin zai taimaka wajen tabbatar da adalci da kuma tsari a harkar zaɓe.
Shugaban kwamitin majalisar wakilai Adebayo Balogun ya ce, gyaran zai rage lokacin yanke hukunci na kotunan zaɓe daga kwanaki 180 zuwa 90, yayin da kotun ɗaukaka ƙara da kotun ƙoli za su yanke hukunci cikin kwanaki 60 da 35.
Ƙarin gyare-gyaren da aka gabatar sun haɗa da tanadin yin zaɓe da wuri ga wasu rukuni na mutane kamar jami’an tsaro, da ƴan jarida, da ma’aikatan hukumar zaɓe da masu sa ido na cikin gida, a ƙalla kwanaki 14 kafin babban zaɓe.
Wakilan hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC), sun nuna goyon bayansu ga wannan shirin.