Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaKungiyar ROTARY ta tallafawa masu bukata ta musamman da kekunan guragu

Kungiyar ROTARY ta tallafawa masu bukata ta musamman da kekunan guragu

Date:

An bayyana masu bukata ta musamman da cewa ba sune sukayi kan su a haka ba duba da yadda wasu suke kyamatar su da kallon su a matsayin nakasasu yayin da suma suna da irin rawar da zasu iya takawa a fanoni daban daban.

Sagam Sanin Ahmad wanda shine shugaban kungiyar ROTARY ta kasa reshen jihar Kano ne  ya bayyana hakan a wajen taron bayar da lambar yabo ga wasu daga cikin ma’aikatan polio d suke bi gida-gida a kasa baki daya da aka gudanar anan Kano.

Sagam ya kuma kara da cewa wannan taron sun yi shine domin karrama wadannan mutane da suka nuna kwazo a lokacin da ke suke aikin yaki da cutar shan inna sannan haka zalika karrmawar zata zamo ta kara musu karfin gwewar gudanar da aikin su.

Shima a nasa bangaren shugaban kungiyar ta Rotary a nan kano cewa yayi wannan kungiyar tasu tana kokarin gani cewa ta bayar da gudunmuwa wajen cigaba da yaki da cutar shan inna a cikin kasar nan dama nan jihar kano dan ganin a kakkabe cutar baki daya kamar yadda aka yaki cutar kyanda baki daya.

Wakilin mu Mustapha Muhammad Kankarofi ya rawaito cewa a yayin taron dai a karrama wanda suka fi kwazo a yayin aikin digon bakin cyaki da cutar ta shan inna inda Jahohin suka hadar da jihar Kano da Katsina Kaduna da kuma jihar Barno.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...