Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar neman diyyar naira miliyan 120 da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir el-Rufai, ya shigar kan DSS da wasu hukumomi uku.
El- Rufa’i ya bukaci biyan diyyar ne bisa zargin sa ido da sauraron wayarsa ba bisa ƙa’ida ba.
Mai shari’a Sylvanus Oriji ne ya yanke hukuncin jiya Litinin, inda ya bayyana cewa ƙarar ba ta da hujjar da za ta sa kotu ta amince da ita.
Kotun ta kuma umarci El-Rufai ya biya kowace daga cikin hukumomin huɗun naira 200,000 a matsayin kuɗin shari’a, waɗanda suka haɗa da DSS, Hukumar EFCC, Hukumar ICPC da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya.
Kotun ta kuma yi watsi da hujjar El-Rufai cewa yunƙurin kama shi ya saɓa wa doka saboda babu sammacin kama shi.
Haka kuma, ta ce kwace fasfo ɗinsa na ƙasashen waje da DSS ta yi ya kasance cikin ikon da doka ta ba hukumar.
