Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya karɓi daftarin kasafin kuɗin Majalisar Ɗinkin Duniya na shekarar 2027, wanda aka kiyasta ya kai kusan dala biliyan 14, daga hannun wakilin dindindin na Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Ambasada Jimoh Ibrahim.
An miƙa wa shugaban ƙasar daftarin mai kundin littattafai guda bakwai a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Lahadi, Jimoh Ibrahim, wanda ke jagorantar kwamitin majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da kasafin kuɗi da harkokin gudanarwa, ya bayyana lamarin a matsayin wani muhimmin tarihi ga Najeriya.
A cewarsa, wannan shi ne karo na farko cikin shekaru 66 da Najeriya ta shugabanci kwamitin da ke da alhakin duba kasafin kuɗin da harkokin gudanarwarta. Najeriya ta fara shugabancin kwamitin ne a ranar 3 ga Satumba, 2026.
