Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da ta cire sunan Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC na kujerar Sanatan Imo ta Yamma a zaɓen 2027.
Kotun ta umarci hukumar da ta maye gurbin sunan Uzodinma da na tsohon gwamnan jihar, Rochas Okorocha.
Mai shari’a Obiora Egwuatu ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa Uzodinma bai lashe zaɓen fid-da-gwani na APC da aka gudanar a ranar 18 ga watan Mayu ba, wanda INEC ta sanya ido a kansa.
Alƙalin ya ce shaidun da aka gabatar a gaban kotu sun nuna cewa Rochas Okorocha ne ya samu mafi yawan ƙuri’u a zaɓen fid-da-gwanin jam’iyyar.
Kotun ta kuma umarci APC da ta miƙa wa INEC sunan Okorocha a matsayin ɗan takararta na kujerar Sanatan Imo ta Yamma a babban zaɓen shekarar 2027.
A halin da ake ciki, INEC ta sanya ranar 16 ga watan Janairun 2027 domin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai
