Gwamnatin Kano ta ce tana samar da fiye da kaso 96 cikin100 na ingantattun duk magungunan da ake buƙata a duka asibitoci mallakin ta, domin sauƙaƙawa al’umma magance kowace cuta a fadin jihar.
Kwamshinan lafiya Dr Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyan hakan, yayin da hukumar samar da magunguna da kayan aikin lafiya ta kano ta buɗe damar karɓar tayin kwangilar kamfanoni domin samarwa da asibitocin gwamnatin Kano magunguna na tsawon shekara 1.
A cewar Dr Labaran daga cikin alfanun baiwa kamfanonin damar ƙulla yarjejeniyar samarwa gwamnati da maganin akwai tabbacin samun magunguna masu inganci da nagarta da sanyawa duk kamfanin da yayi nasara linzamin hana shi ƙarawa gwamnati farashin magungunan sa har na tsawon watanni 6.
Shi ma da yake nasa jawabin. Shugaban hukumar ta samar da magunguna da kayan aikin lafiya a asibitocin Kano Pharmacist Ghali Sule ya ce tsarin shelanta bayar da kwangilar ga kamfanonin maganin, tsari ne da ake amfani da shi a duk duniya, wanda yake taimakawa wajen bunƙasa yawan maganin a asibiti da samun magunguna nagari.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa fiye da kamfanonin siyar da magani 100 ne suka nuna sha’awar ƙulla yarjejeniyar da gwamnatin Kano domin samar da magungunan wanda hakan ya baiwa gwamnati damar tajewa da tsefewa kafin ta aminta da wanda zata yi mu’amala.
Wannan da na turo maka inaso ka fitar min da headline me karfi
