Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce rashin isar da sahihan bayanai kan ayyukan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke gudanarwa a Kano da sauran sassan arewacin Najeriya na daga cikin dalilan da ke sa wasu al’umma ganin kamar gwamnatin tarayya ba ta gudanar da ayyukan raya ƙasa a yankin ba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne yayin wani tattakin nuna goyon baya da ƙungiyar Arewa for Asiwaju ta shirya zuwa gidan gwamnatin Kano, inda ya jaddada muhimmancin wayar da kan al’umma game da ayyukan da gwamnatin tarayya ke gudanarwa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa ta samu nasarori a fannonin gine-gine da kyautata birnin Kano, samar da ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya da sauran muhimman sassa, yana mai jaddada aniyarsa ta ci gaba da samar wa al’ummar jihar romon dimokuraɗiyya.
A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar Arewa for Asiwaju na ƙasa, kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar, ya ce sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu zai taimaka wajen ci gaba da samar da ayyukan more rayuwa da bunƙasa yankin arewacin Najeriya.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa tsohon mataimakin gwamnan Kano, Injiniya Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo, wanda shi ne shugaban ƙungiyar Arewa for Asiwaju a Kano, ne ya jagoranci tattakin daga filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata zuwa gidan gwamnatin Kano.
