Wata babbar koton tarayya a nan kano karkashin mai shari’a Usman Na Abba ta baiwa kamfanin dakon wutar lantarki na kasa TCN umarnin dakatar da shirinsa na rushe wasu gidaje a nan Kano da aka gina su karkashin turakun wutar lantarki.
Hukuncin ya biyo bayan karar da al’ummar unguwannin na Ja’in, Rimin Zakara da Gaida, suka shigar gaban kotun inda suke kalubalantar kamfanin na TCN kan shirin rushe gidajen da suka ce mallakisu ne.
Kan wannan hukunci wakilinmu Mustapha Muhammad Kankarofi ya tattauna da lauyan masu kara Barista Abba Hikima, wanda ya shaida masa cewa, kotun ta yi hukuncin dakatar da rushe gidajen ne zuwa lokacin da za’a yanke hukuncin karshe.
A makon da ya gabata ne dai, a wani taron manema labarai kamfanin na TCN yace ba gudu da ja da bayan wajen rushe gidajen da yace ya biya diyyar gidajen tun a baya.