Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBabu Wata Barazana Da Za Ta Hana Yin Zaben 2023 – Lai...

Babu Wata Barazana Da Za Ta Hana Yin Zaben 2023 – Lai Muhammad.

Date:

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa zabukan 2023, za a yi su kamar yadda aka tsara, don babu wata barazana da zata hana gudanar da shi.

 

Yayin wani taro kan ayyukan da shugaba Buhari ya aiwatar karo na 17, Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce hukumar zabe na hada kai da hukumomin tsaro domin ganin an gudanar da zaben cikin lumana.

 

Da yake tabbatarwa yan kasar nan hakan, Lai Muhammad ya ce hukumomin tsaro na ci gaba da baiwa al’umma tabbacin yin bakin kokarinsu wajen ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

 

A jiya Litinin ne hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC, ta yi gargadin cewa, babban zaben shekarar 2023 na fuskantar babbar barazanar sokewa idan har tabarbarewar tsaro da ta addabi sassan kasar nan bata inganta ba.

Latest stories

Related stories