Saurari premier Radio
24.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiLikitocin Najeriya Za Su Sake Shiga Yajin Aiki.

Likitocin Najeriya Za Su Sake Shiga Yajin Aiki.

Date:

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasa, NARD, ta yi barazanar tafiya yajin aiki, idan gwamnatin tarayya bata biya mata bukatunta ba.

 

Cikin wata wasika da kungiyar ta aikewa ministan lafiya, Dr. Osagie Ehanire, mai dauke da sa hannun shugabanta Dr. Emeka Innocent Orji, tace shirin tafiya yajin aikin zai fara idan ba’a magance matsalolin nasu ba, kafin babban taron majalisar zartarwarsu na kasa, daga 24 ga watan Janairu zuwa 28 ga watan.

 

Tun dai a watannin 6 da suka gabata, kungiyar ta sanya wa’adi kan bukatun mambobin nata da ba’a magance ba, da suka hadar da yin ba dai-dai ba a asusun tallafawa kan baiwa likitocin horo.

 

Sai kuma kudaden alawus-alawus da suke bin bashi na shekarun 2014, 2015 da 2016, da kuma rashin biyan su mafi karancin albashi.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...