Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ci tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola da jam’iyyar ADC tarar Naira miliyan ɗaya saboda neman mai shari’a Peter Lifu ya janye daga sauraron wata ƙara da ake yi.
Mai shari’ar ya bayyana buƙatar tasu a matsayin yunƙurin neman canza alkali domin samun wanda zai yi musu hukunci yadda suke so.
Kotun ta ce ba a gabatar da wata hujja da ke nuna son rai daga ɓangaren alkalin ba, saboda haka ta yi watsi da ƙorafin tare da cin tarar Naira dubu 500 ga kowane ɗaya daga cikin masu neman.
An ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 23 ga watan Yuni domin ci gaba da sauraron sauran buƙatun da ke gaban kotun.
