Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotu ta bada umarnin a kamo dan mai unguwa bisa zargin fasa...

Kotu ta bada umarnin a kamo dan mai unguwa bisa zargin fasa idon wata amarya

Date:

Kotun majistare mai namba 25 wadda mai shari’a Halima Wali ke jagoranta ta umarci mai binciken laifuka na ofishin ‘yan sanda da ke Zango a yankin karamar hukumar Ungogo ya gabatar da wani Ibrahim Kwajalawa cikin sa’o’I 24.

 

Tun farko dai an zargi wasu mutane da laifin fasawa wata amarya Khadija Abdullahi ido yayin bikinta a makon jiya, inda bayan al’amarin ya faru ne ‘yan sanda suka gurfanar da wasu mutane biyu da suka hada da Yahya Adamu, da Salisu Adamu a gaban kotu bisa zargin hada kai da raunata amaryar wanda hakan ya sa ta rasa idota guda daya.

 

Daya daga cikin ‘yan uwan amarya ta shaidawa kotun cewa, akwai dan gidan mai Unguwar cikin wadanda ake zargi, amma jami’an ‘yan sanda sun sallame shi, duk da cewa shi ake zargi da jagorantar matasan da suka aikata lefin.

 

Maishari’a Halima Wali, ta umarci ‘yan sanda su kawo dan mai unguwar cikin nan da awa 24 domin yi wa kowa adalci.

 

Kotun ta aike da sauran mutane biyun zuwa gidan ajiya da gyaran hali, har zuwa lokacin da za a dawo kotun domin ci gaba da sauraron shariar.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...