
Aminu Abdullahi Ibrahim
Rahotanni sun ce Rabiu Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano, ya karbi bakuncin mambobin Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) a ranar Litinin a Abuja.
yayin ganawar an ruwaito cewa Mohammed Bakin, mataimakin shugaban jam’iyyar NDC shiyar arewa maso yamma na cikin manyan shugabannin jam’iyyar da Kwankwaso ya karba a gidansa dake Abuja.
Wata majiya daga kungiyar Kwankwasiyya ta a daren Talata ta ce shugabannin NDC sun nemi Kwankwaso ya shiga jam’iyar kafin zaben 2027.
