Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mai dakin sa, kan abin da ya kira rashin gaggawa wajen tabbatar da sakin ɗalibai da kuma malamai da aka sace a Oyo State.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar, Alhaji Atiku Abubakar ya zargi Gwamnatin Tarayya da mayar da hankali kan harkokin siyasa maimakon ceto waɗanda aka sace.
Ya ce ’yan Najeriya sun yi tsammanin Uwargidan Shugaban Ƙasa za ta fito fili ta yi kira mai ƙarfi domin ganin an kuɓutar da su cikin gaggawa.
Alhaji Atiku ya bayyana cewa, ci gaba da gudanar da tarukan siyasa da bukukuwa yayin da iyalan waɗanda aka sace ke cikin damuwa ya ƙara jawo takaicin a zukutan jama’a.
Ya kuma yi gargaɗin cewa yawaitar sace mutane na iya rage amincewar jama’a ga gwamnati idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba.
Ya buƙaci hukumomin tarayya da su yi amfani da dukkanin ƙarfin tsaro da bayanan sirri domin ceto waɗanda aka sace tare da hukunta masu hannu a lamarin.
