Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da cewa mutane bakwai ne suka rasa rayukansu sakamakon wani sabon rikici da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Darazo.
A sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar yan sandan jihar SP Nafiu Habib, ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:20 na safiyar ranar Alhamis, 4 ga watan Yunin 2026, bayan samun rahoton cewa wasu da ake zargin Makiyaya ne sun kai hari kan wasu manoma da ke sanya takin gargajiya a gonakinsu a garin Lanzai.
Rahotanni sun bayyana cewa rikicin manoma da makiyayan wadda ta samo asali kan taƙaddama filayen noma da hanyoyin burtali, inda da dama suka rasa rayukansu wasu kuma suka samu munanan raunuka sakamakon hare-haren sari-ka-noke dake ɓarkewa tsakanin bangarorin biyu.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani Aliyu, ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan musabbabin rikicin, tare da tabbatar da cewa za a kamo duk wadanda ke da hannu wajan tayar da tarzomar wadda ta laakume rayukan mutane biyar tare da jikkar wasu da dama domin gurfanar da su a gaban kotu.
o
