Hukumar Kwastam ta shirya taron liyafar diflomasiyyar kasa da kasa a birnin tarraya Abuja, da nufin inganta alakar kasuwanci da Ayyukan hukumomin kasa da kasa.
Taron ya gudana a makon nan, a hedikwatar Hukumar Kwastam da ke Abuja, wanda ya samu halartar jakadu, manyan kwamishinoni, shugabannin ofisoshin jakadanci da manyan jami’an gwamnati da nufin ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa, bunƙasa kasuwanci, inganta alaƙar hukumomi.
Da yake jawabi Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam, Adewale Adeniyi MFR, ya jinjinawa abokan hulɗar Najeriya bisa ci gaba da tallafa wa ƙoƙarin ƙarfafa alaƙar diflomasiyya da kuma bunƙasa haɗin gwiwar kasuwanci tsakanin Najeriya da sauran ƙasashe.
Ya kuma ce Hukumar Kwastam na ci gaba da faɗaɗa ayyukanta a matakin duniya ta hanyar tsare-tsaren haɗin gwiwa da hukumomin sama da 20 a faɗin duniya, da nufin musayar ilimi, gina ƙwarewa da haɗin gwiwar ayyuka domin inganta harkokin kasuwanci da kuma kula da iyakoki.
A cewarsa, ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin kwastam, ofisoshin jakadanci da hukumomin tsaro na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da tsaron iyakoki, haɓaka kuɗaɗen shiga ga gwamnati, da ƙara ƙarfin tattalin arzikin ƙasa a cikin yanayin kasuwancin duniya da ke ci gaba da sauyawa.
Taron ya samu halartar Babban Hafsan Sojin Sama na Najeriya, Sufeto Janar na rundunar ‘Yan sanda, mambobin gudanarwar Hukumar Kwastam, da sauran manyan jami’ai daga hukumomin tsaro da na gwamnati da sauran mambobi daga ciki da wajan kasar nan.
