Gwamnatin Kano ta ce nan bada jimawa za ta kammala ayyukan magudanan ruwa da hanyoyin da suke yankunan da zaizayar kasa ke illatawa musammanma a lokacin damuna.
Kwamishinan Ma’aikatar Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi ta jihar Dr. Dahiru M Hashim ne ya bayyana hakan a yayin wata ziyara da ya kai Unguwar Getsi da ke Rimin Kebe domin duba aikin daya hada hanyar Getsi zuwa Gayawa Bulbula.
Kwamishinan ya yaba da yadda Injiniyoyi da sauran ma’aikata ke gudanar da aikin cikin sauri da kuma inganci, inda ya ce aikin babbar hanyar wani babban kundi ne da ya hadar da fadada babbar kwatar da ke yankin da samar da Gadoji guda 5 domin inganta al’ummar yankin da kuma dakile ambaliyar ruwa da suke fuskanta.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Hashim na umartar ‘yan kwangilar aikin da su kara zage dantse wajen yin nagartaccen aiki tare da bukatar yankunan da lamarin zai shafa da su bada cikakken hadin kai da goyon baya domin samun nasarar aikin.
