Gwamnatin Kano ta kaddamar da aikin yashe babbar kwatar Jakara zuwa Kwarin Gogau tare da sauran manyan magudanan ruwa dake yankin, a wani mataki na shirin hana afkuwar ambaliyar ruwa yayin da ake shiga daminar bana.
Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr Dahiru M. Hashim, ne ya kaddamar da aikin, inda ya bayyana cewa shirin wani bangare ne na kudurin gwamnatin Kano na kare rayuka da dukiyoyin al’umma daga illar ambaliyar ruwa.
Dr Hashim ya ce za’a gudanar da aikin ne a wuraren da aka fi fuskantar matsalar taruwar ruwa da ambaliya, yana mai jaddada cewa gwamnatin kano ta himmatu wajen samar da mafita mai dorewa ga matsalolin muhalli da suka addabi wasu sassan Kano.
Kwamshinan ya ce aikin ba wai kawai zai taimaka wajen saukaka kwararar ruwa ba ne, zai kuma taimaka wajen kare hanyoyi, makarantu, gidaje da sauran muhimman ababen more rayuwa daga lalacewar da ambaliya ke haddasawa a duk shekara.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Hashim na yin kira ga mazauna Kano da su guji zubar da shara a magudanan ruwa tare da kiyaye muhalli, yana mai cewa gwamnati ba zata samu nasarar da take ba sai ta samu hadin kai tsakanin ta da al’umma.
