Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya umarci hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na Najeriya EFCC da ICPC da su sanya ido kan rabon takin zamani mai rangwame da gwamnatin sa ta tanadarwa manoman jihar.
Gwamna Abba ya bayar da umarnin ne yayin kaddamar da rabon motocin tirela 150 dauke da takin zamani wanda za a siyarwar manoma jihar akan farashi me rangwame.
Gwamnan ya ce sanya hukumomin yaki da cin hanci cikin shirin zai tabbatar da ganin takin ya isa hannun manoma na gaskiya tare da dakile karkatar da shi ko boye shi domin amfanin wasu tsiraru.
Gwamna Abba ya ce manufar shirin ita ce rage tsadar noma, kara yawan amfanin gona da kuma inganta wadatar abinci, tare da yin gargadin cewa duk wanda aka samu da laifin karkatar da takin ko kawo cikas ga shirin zai fuskanci hukunci bisa tanadin doka.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito gwamna Yusuf na bukatar shugabannin kananan hukumomi 44 na jihar, da su gudanar da rabon cikin gaskiya, adalci da rikon amana.
