Jihohin Najeriya 36 sun karɓi jimillar kuɗi har naira tiriliyan 4.83 daga asusun rarraba kuɗaɗen gwamnatin tarayya, FAAC, a cikin watanni shidan farko na shekarar 2026, wato daga janairu zuwa yuni.
Binciken rabon kuɗaɗen ya nuna cewa jihohin sun karɓi jimillar Naira tiriliyan 4.832,229,131,576.51 a wannan lokaci, inda jihar Delta ta fi sauran jihohi karɓar kuɗi, sai Legas, Rivers, Akwa Ibom da Bayelsa.
Jihar Delta ta karɓi kusan Naira biliyan 369.87, yayin da Legas ta samu Naira biliyan 368.79. Jihar Rivers ta zo ta uku da Naira biliyan 331.73, sai Akwa Ibom da Naira biliyan 300.73, sannan Bayelsa da Naira biliyan 289.19.
Wani bincike da cibiyar Agora Policy ta gudanar ya nuna cewa jimillar kuɗaɗen da aka raba wa jihohi a watannin farko na shekarar nan ya kai Naira tiriliyan 4.47, idan aka yi la’akari da rabon da aka bayyana a nazarinta kan kuɗaɗen FAAC.
Rabon kuɗaɗen FAAC na daga cikin manyan hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ga gwamnatocin jihohi, waɗanda suke amfani da su wajen gudanar da ayyukan gwamnati, biyan albashi da samar da ayyukan more rayuwa, sai dai yawan kuɗin da jiha ta karɓa shi kaɗai ba ya nuna yadda ta kashe kuɗin ko irin ayyukan da ta aiwatar.
