Wani mazaunin unguwar Ɗanbare da ke nan Kano, Ibrahim Yusuf, ya bayyana irin baƙin cikin da yake ciki bayan rasuwar ’ya’yansa biyar cikin kwanaki takwas, sakamakon wata cuta da ake zargin cutar mashako ce, wadda ke ci gaba da haifar da damuwa a jihar.
Yusuf ya ce lamarin ya fara ne bayan yaran sun fara fama da zazzaɓi, inda ya kai su cibiyar kula da lafiya a matakin farko da ke Kabuga, daga baya, yayin da yanayinsu ya tsananta, aka tura su asibitin kula da cututtuka masu yaɗuwa, wato IDH, da domin samun kulawa ta musamman.
A cewarsa, yara biyu sun rasu a rana guda, saura uku kuma suka rasu a cikin kwanakin da suka biyo baya, ya bayyana sunayen yaran a matsayin Sadiq mai shekara 13, Aisha da Zainab masu shekara bakwai, Umar mai shekara shida, da Aliyu mai shekara ɗaya da rabi.
Daily trust ta rawaito cewa wani ma’aikacin hukumar kula da cututtuka ta jihar Kano, KNCDC, ya tabbatar da rasuwar yaran biyar, duk da cewa hukumar ba ta bayar da cikakken bayani a hukumance ba a lokacin da aka wallafa rahoton, wani rahoto dabam ya ce har yanzu ana gudanar da bincike domin tabbatar da ainihin musabbabin rasuwar yaran.
Ibrahim Yusuf ya yi kira ga gwamnati da hukumomin lafiya da su ƙara ƙaimi wajen dakile yaɗuwar cutar da kuma wayar da kan al’umma, masana lafiya sun jaddada muhimmancin yin allurar rigakafi, kai masu alamun cutar asibiti da wuri, da kuma guje wa jinyar cutar a gida ba tare da kulawar ƙwararru ba.
