Jagoran ɗariƙar ƙadiriyya na Ƙasa, Sheikh Qaribullah Sheikh Nasiru Kabara, ya ziyarci Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, a Abuja, inda ya yaba da nasarorin da gwamnatinsa ke samu tare da yi masa addu’ar samun ƙarin hikima da lafiya wajen ci gaba da jagoranci.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, inda sanarwar ta ce ziyarar ita ce irinta, ta farko a hukumance tsakanin jagororin biyu.
Sheikh Qaribullah ya yabawa Gwamna Yusuf kan ci gaban da gwamnatinsa ta samu musamman a fannonin ababen more rayuwa, ilimi da lafiya, tare da ƙarfafa masa gwiwar ci gaba da aiwatar da manufofin raya Kano.
Ya kuma tabbatarwa da gwamam cewa, mabiya ɗariƙar Ƙadiriyya zasu masa ci gaba da addu’o’i domin zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Kano da Najeriya baki ɗaya.
A nasa jawabin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gode wa Sheikh Qaribullah bisa ziyarar, inda ya ce hakan alama ce ta kyakkyawar alaƙa tsakanin gwamnati da shugabannin addini, tare da ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da manufofin da suka shafi jin daɗin al’umma da kuma ɗorewar ayyukan ci gaba a faɗin Jihar Kano.
