Saurari premier Radio
24.5 C
Kano
Saturday, July 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiIPMAN ta bayyana rikicin Isara'ila da Iran a matsayin babban dalilin ƙarancin man fetur.

IPMAN ta bayyana rikicin Isara’ila da Iran a matsayin babban dalilin ƙarancin man fetur.

Date:

Kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN, ta bayyana rikicin Isra’ila da Iran a matsayin babban dalilin karancin man fetur da ake fama da shi a kasar nan.

A wata hira da gidan talabijin na ARISE, Sakataren kungiyar na kasa, James Tor, ya bayyana irin rawar da gwamnatin tarayya ke takawa wajen shigo da albarkatun man fetur da kuma ware su ga masu ruwa da tsaki ciki har da kungiyar IPMAN domin rabawa.

Ya yi nuni da cewa, tashe-tashen hankulan da ake fama da su a yankin Gabas ta Tsakiya a halin yanzu, sun ƙara taɓarɓarewar ƙalubalen da ake fuskanta, wanda ya haifar da cikas a harkar samar da kayayyaki.

Sai dai ya ce kamfanin man na asa NNPC ya kara himma wajen ganin an shawo kan lamarin ta hanyar buɗe gidajen man fetur domin tabbatar da wadatuwarsa a faɗin ƙasar nan.

Matsalar karancin man fetur na kara tsanani musamman a manyan birane, a daidai lokacin da kungiyar dillalan man da kamfanin NNPC ke ci gaba da fitar da bayanai dake sabawa juna a kan matsalar.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...