A karon farko tun bayan ɓarkewar yaki tsakanin Amurka da Iran, Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya isa birnin New York na Amurka domin halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 81, yayin da ake cigaba da samun takun-saka tsakanin Tehran da Washington.
Araghchi ya isa New York ne bayan ya yi ɗan takaitaccen zama a Doha, kuma ana sa ran zai gana da ministocin harkokin wajen wasu ƙasashe da jami’an gwamnati a yayin taron.
Ziyarar tasa na zuwa ne yayin da rikicin da ya shafi Iran, Amurka da Isra’ila ke cigaba da yin tasiri kan taron Majalisar Dinkin Duniya.
Iran ta ce za ta yi amfani da taron domin bayyana matsayinta tare da kare abin da ta kira haƙƙoƙi da muradun al’ummarta.
Bayan isarsa New York, Araghchi ya kuma yi wata tattaunawa ta waya da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres.
An ce sun tattauna batutuwan da suka shafi ajandar taron Majalisar Dinkin Duniya da kuma zaman lafiya da tsaro a duniya.
Ana sa ran shima Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, zai isa New York a yau Talata domin gabatar da jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya.
Har ila yau, Pezeshkian zai gana da shugabannin ƙasashe da wasu jami’an gwamnati a gefen taron.
Ziyarar tawagar Iran na zuwa ne bayan da Amurka ta amince ta ba wasu manyan jami’an Iran, ciki har da Pezeshkian da Araghchi, biza domin halartar taron.
Sai dai Washington ta sanya takunkumi kan zirga-zirgarsu a wasu sassan birnin New York, yayin da aka ruwaito cewa wasu daga cikin tawagar Iran, ciki har da wasu ma’aikatan kafafen yaɗa labarai na shugaban ƙasar, ba a ba su biza ba.
Matakin ya ƙara janyo rashin jituwa tsakanin ƙasashen biyu a lokacin da ake ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyya a yayin rikicin.
