Hukumomin Bangladesh sun hana yin layya da wani farin bijimin sa mai ban mamaki da aka yi wa lakabi da Donald Trump saboda gashin kansa mai launin ruwan zinariya, bayan matakin gaggawa da gwamnati ta ɗauka kafin Babbar Sallah.
Rahotanni sun bayyana cewa an sanya wa dabbar sunan shugaban Amurka Donald Trump ne saboda irin gashin kansa da ke kama da nasa.
Ma’aikatar Cikin Gida ta Bangladesh ta tabbatar a ranar Laraba cewa, saboda dalilai na tsaro an kai dabbar a gidan ajiye dabbobi domin ci gaba da kula da shi.
