Ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya a Najeriya sun kashe sama da naira biliyan 50 da miliyan 410 kan tafiye-tafiyen ƙasashen waje, tikitin jirgi, kuɗaɗen estacode da alawus-alawus, da kuma horaswa a ƙasashen waje cikin shekaru uku.
Wani bincike da jaridar Leadership ta wallafa, bisa bayanan biyan kuɗaɗen gwamnati da dandalin GovSpend ya tattara, ya nuna cewa an kashe kuɗaɗen ne tsakanin watan Yunin 2023 zuwa 19 ga Yunin 2026, ta hanyar ma’amaloli guda dubu 1,967 daga hukumomin gwamnati 129.
Binciken ya nuna cewa kuɗin tikitin jiragen sama na ƙasashen waje sun kai naira biliyan 23 da miliyan 700, yayin da kuɗaɗen estacode da alawus-alawus suka kai biliyan 17 da miliyan 50. Sauran kuɗaɗen masauki, biza, rajista da sauran hidimomin tafiye-tafiye sun kai biliyan 5 da miliyan 350.
Hukumar Technical Aid Corps ce ta fi kowace hukuma kashe kuɗi a cikin bayanan da aka bincika, inda ta kashe naira biliyan 11 da miliyan 700 a ma’amaloli 93. Ofishin Akanta-Janar na Tarayya ya biyo baya da biliyan 5 da miliyan 160, yayin da hedikwatar fadar shugaban ƙasa ta kashe biliyan 4 da miliyan 830.
Sai dai rahoton ya bayyana cewa adadin naira biliyan 50 da miliyan 410 ƙiyasin mafi ƙarancin kuɗin da aka kashe ne, saboda binciken ya fi mayar da hankali kan biyan kuɗaɗen da suka kai naira miliyan biyar ko sama da haka. Hakan na nufin ba’a haɗa wasu ƙananan kuɗaɗen tafiye-tafiye cikin jimillar ba.
