Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiHukumar NDLEA Ta Kaddamar Da Sabon Shirin Yaki Da Miyagun Kwayoyi Na...

Hukumar NDLEA Ta Kaddamar Da Sabon Shirin Yaki Da Miyagun Kwayoyi Na “OPERATION HANA MAYE’’ A Jihar Kano

Date:

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Kano, ta kaddamar da wani sabon shiri mai suna “OPERATION HANA MAYE” da nufin yaki da safara da shan miyagun kwayoyi a jihar.

Karkashin shirin hukumar ta kadammar da samame a filin wasa na Sani Abacha a ranar Larabar da ta gabata inda ta yi nasarar chafke mutum 58 da kayan maye daban-daban.

Kwamandan hukumar, Abubakar Idris Ahmad, ya bayyanawa Premier radio cewa sun kaddamar da wannan shirin sakamakon yawan korafe-korafen da suke samu daga al’umma game da karuwar yawan ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Kwamandan ya kuma ce da zarar sun kama mutum za a yanke masa hukunci ne nan take bayan gudanar da bincike.

Kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyin, ya ce ba za su gajiya ba har sai sun ga al’umma jihar Kano sun daina ta’ammali da miyagun kwayoyin.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...