Hukumar yaƙi da cin Hanci da rashawa ta ICPC a Najeriya, ta ce tana shirin shigar da darussan yaƙi da cin hanci da rashawa cikin manhajar Makarantar Horar da Lauyoyi ta kasar, domin samar da ƙwararrun lauyoyi masu riƙon amana, gaskiya da mutunta doka.
Shugaban hukumar, Dr Musa Adamu Aliyu SAN ne ya bayyana haka a wajen rufe taron bitar da ICPC ta shirya haɗin gwiwa da Makarantar Horar da Lauyoyi a Abuja.
Dr Musa ya ce ilimantarwa na daga cikin manyan hanyoyin da za su taimaka wajen rage cin hanci da rashawa, domin hukunta masu laifi kaɗai ba zai magance matsalar gaba ɗaya ba.
A cewar sa lauyoyi na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da adalci, saboda haka koyar da su ƙa’idojin yaƙi da cin hanci da rashawa tun suna makaranta zai taimaka wajen inganta ɗabi’a da ƙwarewa a fannin shari’a.
A nasa jawabin, tsohon shugaban Makarantar Horar da Lauyoyi ta Najeriya, Farfesa Isa Hayatu Chiroma, SAN, ya ce mahalarta taron sun duba daftarin manhajar da ƙwararru suka tanada, inda ya ce za’a tattara shawarwarin waje guda, kafin Hukumar kula da Ilimin Shari’a, Makarantar Horar da Lauyoyi, shugabannin tsangayoyin koyar da shari’a, ICPC da sauran masu ruwa da tsaki su tantance ta, kafin a fara aiwatar da shirin a faɗin Najeriya.
