Gwamnatin Jihar Zamfara ta dakatar da wasu ayyukan yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC da aka shirya gudanarwa a Ƙaramar Hukumar Maru, sakamakon hatsarin mota da ya yi sanadin mutuwar magoya bayan jam’iyyar 15.
Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 da rabi na ranar Litinin, 23 ga Nuwamban 2026, kusa da ƙauyen Kisami, a kan hanyar Gummi zuwa Anka, yayin da magoya bayan APC ke tafiya zuwa Talata Mafara domin halartar taron yaƙin neman zaɓe.
Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa, FRSC, ta tabbatar da cewa mutane 15 sun mutu, yayin da wasu 27 suka jikkata. Mutane 10 kuma sun tsira ba tare da rauni ba.
Rahoton hukumar ya nuna cewa hatsarin ya shafi motoci biyu, ƙirar Toyota Camry da babbar motar Mitsubishi Canter. An bayyana yin ƙetare mota ba bisa ƙa’ida ba da kuma rasa ikon sarrafa abin hawa a matsayin abubuwan da ake zargin sun haddasa hatsarin.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na Zamfara, Mahmud Dantawasa, ya sanar da dakatar da ayyukan yaƙin neman zaɓen a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Gusau.
Ya bayyana alhinin gwamnatin jihar, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda
