Kafofin yaɗa labaran gwamnatin Rasha sun bayar da rahoton cewa mutum biyu sun mutu sakamakon hare-haren jiragen sama marasa matuƙa da Ukraine ta kai birnin Moscow.
Rahotannin sun ce hare-haren sun kuma lalata wasu sassan matatar man fetur ta Moscow, lamarin da ya haifar da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na wani lokaci.
Magajin garin Moscow ya ce an dakatar da zirga-zirgar jiragen sama sama da 30, yayin da ya zargi Ukraine da kai hare-haren da nufin yin tasiri kan zaɓen majalisar dokokin Rasha.
Hare-haren sun faru ne a jajibirin zaɓen majalisar dokokin ƙasar.
Wannan na zuwa ne duk da cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce a makon da ya gabata Rasha da Ukraine sun amince da dakatar da kai hare-hare kan wuraren samar da mai na juna.
An cimma yarjejeniyar ne yayin da ake ci gaba da fuskantar matsin lamba kan samar da man fetur da makamashi a duniya.
