
Aminu Abdullahi Ibrahim
Ana zargin wani mahaifi mai suna Alhaji Yunusa da akewa lakabi da Ale Malam ya rafke malaman makarantar da ‘ya’yansa ke karatu da Gora.
Lamarin ya faru ne a unguwar Tukuntawa hayin diga bayan sallar Magriba ranar Laraba.
Tun da fari dai daliban na karatu ne a wata makarantar dare mai suna Tasbitul-Uqul Tukuntawa.
A cewar shugaban makarantar ‘ya’yansa biyu sun yi laifi na batar da Tabarma sakamakon hukunta su da akayi sai mahaifinsu Ale Malam ya dauko gora inda ya rinka bin Malaman makarantar yana duba lamarin da ya sa suka nemi tsira.
Wani shaidar gani da ido yace suna tsaye a gefen masallacin da Islamiyar take sai suka ga mutum da Gora yana yana dukan mutane a cewarsa nan da nan suka kira mutane domin Kai musu dauki.
Ya ce a nan ne suka fahimci hakikanin abinda ya faru. Ya ce ya jiwa wasu daga cikin su ciwo a kai sakamakon duka.
Tuni dai jami’an ‘yan sanda dake Sharada suka kama mutumin.
