KNGH/MUHALLI
Gwamnatin tarayya ta buƙaci sauran jihohin Najeriya su yi koyi da ƙoƙarin Gwamnatin Kano take yi wajen yin dashen bishiyoyi da farfaɗo da Muhalli domin magance kwararowar Hamada da ɗumamar yanayi.
Ministan Muhalli Alhaji Balarabe Abbas Lawal ne ya bayyana haka, yayin bikin ranar kare kandagarkin Hamada ta shekarar 2026, da ƙaddamar da shirin dashen bishiyoyi na bana, da kuma miƙa sabon ofishi ga Hukumar kula da kandagarkin Hamada ta Ƙasa a Kano
Ministan ya ce Kano ta zama abin koyi a Najeriya wajen yaƙi da sauyin yanayi, tare da tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da marawa jihar baya domin faɗaɗa ayyukan bunƙasa muhalli, da yin kandagarkin kwararowar Hamada.
A nasa jawabin, Kwamishinan albarkatun ruwa, muhalli da sauyin yanayi na Kano, Dr Dahiru M Hashim, ya ce dawo da Shakwatar Hukumar ta ƙasa zuwa Kano babban ci gaba ne ga manufofin kare muhalli a Najeriya, tare da tabbatar da cewa gwamnatin Kano za ta samar da goyon bayan da hukumar ke buƙata domin sauke nauyin da ke kanta.
Dr Dahiru ya ce gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta samar da kyakkyawan tsarin kula da sauyin yanayi, kuma tuni aka fara aiwatar da su, wanda hakan ya ɗaga matsayin Kano a fannin tafiyar da harkokin sauyin yanayi daga 34 a shekarar 2024 zuwa matsayi na huɗu a shekarar 2025.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Hashim na cewa gwamnatin Kano ta dasa miliyoyin bishiyoyi, tare da farfaɗo da fiye da hekta dubu hamsin na ƙasar da ta lalace, tare da yabawa Hukumar bisa tallafin shukar dabino dubu dari biyar da ta baiwa Kano domin ƙarfafa samar da abinci, ayyukan yi da kuma rage illar sauyin yanayi.
