Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙasar Faransa domin bunƙasa harkokin noma, ilimi, albarkatun ruwa, sabunta makamashi da kare muhalli a jihar.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, inda sanarwar ta ce Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne yayin bikin raanar ƙasar Faransa da aka gudanar a ofishin jakadancin ƙasar da ke Abuja.
A yayin taron, gwamnan ya taya gwamnatin Faransa da al’ummarta murnar ranar Ƙasa, tare da yabawa da daɗaɗɗiyar alaƙar da ke tsakanin Najeriya da Faransa, inda gwamnan ya ce haɗin gwiwar dake tsakanin ƙasashen biyu ta daɗe tana taimakawa wajen bunƙasa ci gaba da fahimtar juna tsakanin su.
Gwamna Abba ya ce gwamnatin Kano za ta ci gaba da aiki tare da ƙasashe da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa domin jawo hankalin masu zuba hannun jari, domin inganta ayyukan gwamnati da kyautata rayuwar al’ummar Kano.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa Gwamna Abba ya kuma bayyana cewa ƙarfafa alaƙa da ƙasar Faransa zai samar da sabbin damammaki a fannonin fasaha, musayar ƙwarewa da ci gaba mai ɗorewa a Kano.
